✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashiya ta rasu a zanga-zangar kafa kasar Yarbawa

An ruwaito cewa harsashi ne ya kubuce ya yi ajalin matashiyar.

Wata matashiya ta gamu da ajalinta lokacin da harsashi ya kubuce ya same ta a yankin Ojota na Jihar Legas, yayin zanga-zangar nema kafa kasar Yarbawa a ranar Asabar.

Mazauna yankin da suka shaida faruwar lamarin sun ce harsashin ‘yan sanda ne ya kubuce ya kashe ta, a yunkurin da suke yi na tarwatsa masu zanga-zangar.

  1. Abin da ya sa na cire dana daga makarantar gwamnati – El-Rufa’i
  2. Ma’aikatan Katsina sun koka kan zaftare musu albashi

Wata da ta gane wa idonta abin da faru ta ce matashiyar mai suna Jumoke ta gamu da ajalinta ne a kan hanyar zuwa shagon da take sayar da kayan sanyi.

Wani gungun masu zanga-zangar da ake yiwa lakabi da ‘Ilano Omo O’dua’ daga yankin Kudu Maso Yamma sun zabi jihar Legas don gudanar da zanga-zangar.

Wanda ya fara kitsa zanga-zangar shi ne Sunday Igboho.

Umarnin Sunday Igboho

Igboho, wanda ya sanar da fasa zanga-zangar bayan jami’an DSS sun kai samame gidansa, ya yi mi’ara-koma-baya inda ya sake cewar za su fito don yin gangamin.

Ya umarci magoya bayansa su yi fitar tsinke yayin zanga-zangar duk da kashedin jami’an ‘yan sanda.

Amma a ranar Asabar, jami’an tsaro sun datse hanya tare da rufe inda za a gudanar da zanga-zangar, wadda daga bisani ta rikide zuwa tashin hankali.