✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashiya ta yi karar Mahaifinta saboda kin aura mata wanda take so

Saurayinta bai kammala cika duka sharudan aure ba.

Wata matashiya mai suna Halima Yunusa ta yi karar mahaifinta a wata Kotun Shari’ar musulunci da ke Jihar Kaduna kan zargin kin aura mata masoyinta mai suna Bashir Yusuf.

Kamfanin Dilancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa Halima ta shaida wa kotun cewa tana matukar son Bashir amma iyayenta sun ki yarda su aura mata shi.

Mahaifin mai suna Ibrahim ya shaida wa kotun cewa yana sane da irin soyayyar da ke tsakanin ’yarsa da Bashir, amma a cewarsa, Bashir bai kammala cika duka sharudan aure ba.

Mahaifin ya yi ikirarin cewa ya fada wa saurayin ’yarsa da ya turo iyayensa amma kusan shekara guda bai yi hakan ba.

“Sai bayan shekara guda ya zo ya dauki ’yar suka tafi har kwana uku ba su dawo ba

“Daga baya muka samu labarin cewa sun dawo sun tafi gidan wata ’yar uwata,” a cewar mahaifin Halima.

“Sai muka sanar da ’yan sanda wanda a sanadiyar haka suka shiga hannu.

“Bayan sun fito daga komar ’yan sandan sai suka sake guduwa Abuja inda suka shafe tsawon makonni biyu.

Mahaifin Halima ya ce daga baya ya hadu da mahaifin Bashir inda har mahaifin Yusuf din ya gargade shi kan cewa ba zai yarda dansa ya auri ’yarsa ba.

“A karshe dai sai da hakan ta kai mu har gaban Mai garin kauyenmu, inda aka kulla yarjejeniya kuma kowannenmu ya sa hannu a gaban shaidu cewa na gargadi ’yata a kan ta rabu da dansa.”

Sai dai Bashir ya shaida wa kotun cewa yana matukar kaunar Halima, wanda kotun ta shawarci mahaifinsa a kan ya bari a daura musu aure.

Sai dai bayan sauraron duka bangarorin, Alkalin Kotun, Murtala Nasir ya bayar da umarnin cewa mahaifin Yusuf ya bari dansa ya auri Halima idan kuma bai bari ba kotun za ta daura musu aure.

Ya kuma shawarci Halima ta nemi gafarar iyayenta domin samun tabarraki a rayuwarta, inda ya dage zaman kotun zuwa ranar 23 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.