Daily Trust Aminiya - Matatar Dangote za ta rika fitar da fetur zuwa Turai
Subscribe

Daga dama Aliko Xangote da Minista Timipre Sylva da Shugaban Kamfanin NNPC Injiniya Kolo Kyari

Matatar Dangote za ta rika fitar da fetur zuwa Turai

Rukunin Kamfanonin Dangote ya ce yana shirin zai fitar da tataccen man fetur daga matatar kamfanin zuwa Turai da Kudancin Amurka da Afirka ta Yamma da kuma Tsakiyar Afirka da zarar an kammala ta.

Kamfanin ya bayyana haka ne a  ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da ayarin Minista a Ma’aikatar Man Fetur Cif  Timipre Sylba ya kai ziyarar aiki a matatar da ake ginawa a Jihar Legas.

Daraktan Tsare-Tsare da Manyan Ayyuka da Ci gaba na Kamfanin Dangote, Mista Debakumar Edwin ya ce, matatar tana da karfin tace gangar danyen mai dubu 650, a kullum, don haka za a iya fitar da tataccen man zuwa ko’ina a fadin duniya.

Ya ce “Yana daga cikin burinmu fitar da man dizal zuwa kasashen Turai, mun tanadi kayan aiki da za mu aiwatar da wannan kudiri namu. Sannan za mu fitar da rarar man fetur zuwa Kudancin Afirka bayan wanda za mu fitar zuwa Yammaci da Tsakiyar Afirka. Wannan ya sa muka yanke shawarar shiga kasuwannin Turai.

Matatarmu za ta iya tace duk man da ake hako shi a Najeriya da sauran kasashen Afirka,” inji shi.

Ya ce matatar za ta wadatar da dukkan bukatun Najeriya a bangaren albarkatun mai, kuma za a samu rarar da za a fitar zuwa kasashen ketare.

Bayan kammala zagayen matatar, Ministan ya ce “Wannan aiki ne mai matukar burgewa, kuma wannan shi ne aiki mafi ban sha’awa, wanda dan asalin  Najeriya yake yi. Lallai wannan ci gaba ne  mai karfafa gwiwa, mun yanke shawarar taimaka wa wannan aiki. Taimakon da gwamnati  za ta yi, ya hada da samar wa matatar danyen man fetur da kuma ganin ta fara aiki,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Gwamnati za ta bada tabbacin haka, amma wannan ya dogara ne ga yadda tattaunawa za ta kasance tsakanin Aliko Dangote da Gwamnatin Tarayya. Da zarar kamfanin ya mika kudirinsa ga gwamnati za mu duba mu ga irin gudunmawar da za mu bayar.”

Shugaban Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya “Idan ba mu yi wannan aiki ba babu wanda zai zo ya yi mana sai dai mu. Ya kamata a ce  Najeriya tana ciyar da Yammacin Afirka da Tsakiyarta, kuma wannan shi ne abin da yake gabanmu. Shi ya sa muke wannan katafaren aiki.”

More Stories