✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matawalle ya dakatar da hukumar ZAROTA

Gwamnan ya dakatar da hukumar biyo bayan korafin cin zarafin mutane da jami'anta ke yi.

Gwamnan Zamfara, Bello Muhammed Matawalle, ya dakatar da Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar (ZAROTA).

  • Sakataren Gwamnatin Jihar, Yakubu Sani Haidara ne, ya sanya hannu a jawabin da aka fitar na dakatar da Hukumar, bayan korafe-Korafen al’umma game da ayyukansu a jihar.
  1. FGC Yauri: An kashe dan sanda, an sace malamai da dalibai
  2. ’Yan bindiga sun kashe mutum 26 a kauyen Zamfara

“Daga yanzu hadin gwuiwar jami‘an ’yan sandan, VIO, hukumar kiyaye hadura da na ‘Civil Defence’ ne za su ci gaba da aikin hukumar.

“Mai Girma Gwamna ya kuma ba da umarnin bincike kan hukumar da jami’anta.

“Saboda haka ana umartar jama’a da su kasance masu bin doka,” a cewar jawabin.

A ranar Alhamis ne direbobin manyan motoci suka tare babbar hanyar Gusau zuwa Zariya, suna zanga-zanga kan kudaden da suke zargin jami’an hukumar ke karba a hannunsu.

Matafiya da dama ciki har da daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau sun samu tsaiko sakamakon tare hanyar.

Shugabannin masu manyan motocin sun ce sun yi hakan saboda abun da suka kira irin cin zarafi da jami’an na  ZAROTA ke yi wa mambobinsu.

An kirkiro hukumar a lokacin mulkin gwamna Abdulaziz Yari, don rage cunkoson ababen hawa a jihar.

Amma daga bisani an dinga shigar da korafi kan yadda hukumar ke amfani da karfin iko wajen cin zarafin mutane a jihar.