✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle ya kori Kwamishinan Kudin Zamfara

An tsige Kwamishinan bayan samunsa da laifin yi wa gwamnatin Jihar zagon kasa.

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara, ya amince da dakatar da Aliyu Tukur a matsayin Kwamishina a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta jihar.

An soke nadin nasa ne biyo bayan tabbatar da sa hannunsa cikin ayyukan da za su iya bata sunan gwamnatin Jihar Zamfara kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a kwanakin baya an gurfanar da kwamishinan a gaban kotu bisa wasu ayyukan zagon kasa da ka iya zubar da kimar Gwamnatin Gwamna Bello Matawalle.

An bukaci tsohon kwamishinan da ya mika duk wasu takardu da kadarorin gwamnatin da ke hannunsa ga Babban Sakataren ma’aikatarsa.

Wannan na zuwa ne biyo umarnin da gwamnan ya bayar na korar kungiyoyi masu zaman kansu a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce ta gano wasu daga cikin kungiyoyin da hannu wajen rura wutar matsalar rashin tsaro a jihar da makotanta.