✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle ya nemi afuwar kafofin yada labaran da ya rufe

Gwamnatin Zamfara ta aike da takardar ban hakuri ga gidajen talabijin da radiyo da ta rufe.

Gwamnatin Zamfara ta ba da hakuri kan matakin rufe wasu kafafen yada labarai a jihar, wanda ya ja mata Allah wadai.

Kafofin yada labaran da lamarin ya shafa sun hada da tashar NTA da gidan Pride FM da ke Gusau, baki dayansu mallakar mallakin Gwamnatin Tarayya.

Sai kuma tashar Gamji TV da Gamji FM da Al-umma TV wadanda suke masu zaman kansu.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar, ta nuna kafofin da aka rufen sun saba wa dokar jihar da ma ta aikin jarida, shi ya sa aka dauki matakin a kansu.

A ranar Litinin aka ga jigo a gwamnatin jihar, Dokta Abdullahi Shinkafi, ya mika wa tashoshin da lamarin ya shafa takardar ban-hakuri a madadin gwamnati, a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Gusau.

Dokar da gwamnatin ta ce an take, ita ce wadda ta haramta tarurrukan siyasa a jihar saboda dalilai na tsaro.