Matawalle ya raba wa Sarakunan gargajiya 260 motoci na alfarma a Gusau | Aminiya

Matawalle ya raba wa Sarakunan gargajiya 260 motoci na alfarma a Gusau

    Ishaq Isma’il Musa da Shehu Umar, Gusau

Gwamna Bello Mohammed Matawalle, ya raba wa duk masu rike da masarautun gargajiya 260 motoci na alfarma a Jihar Zamfara.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya bude babbar hedikwatar Majalisar Malamai ta jihar a Yammacin ranar Laraba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III shi ne ya jagoranci rabon motocin wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

Sarkin Musulmin ya yaba wa Gwamna Matawalle dangane da yadda ya riki inganta jin dadin masarautun gargajiya da muhimmanci, wanda a cewarsa har yanzu su ne ginshikin hadin kan al’umma.

Ya yi kira ga Sarakunan gargajiyar da su ci gaba da bai wa Gwamna Matawalle goyon bayan da ya dace musamman a fafutikar da gwamnatinsa take yi na ganin ta kawo karshen kalubalen da al’umma ke fuskanta a jihar.

A nasa bangaren, Gwamna Matawalle ya ce wannan tagomashi na da madogara da yadda sarakunan gargajiyar suka zamanto wani tubali kuma jakadu na addini da al’ada wadanda ya ce su ne kashin bayan hadin kai da zaman lafiya a kowacce al’umma.

“A dalilin haka ne gwamnatina ta ke martaba sarakunan gargajiya da kuma masarautunsu.

“Wannan ya sa muka ga ya dace mu sayo musu sabbin motoci na alfarma don inganta walwala da jin dadinsu.

“Mun siya musu sabbin motoci samfurin Cadillac kirar 2019, wadanda za a raba wa Sarakuna 17, Iyayen Kasa 13 da kuma Dagatai 230 da ke fadin jiharmu,” a cewar Gwamnan.

Motocin da Gwamna Matawalle ya raba wa Sarakunan gargajiya a Zamfara.

Kadan daga cikin motoci samfurin Cadillac kirar 2019 da Gwamna Matawalle ya raba wa Sarakunan gargajiya a Zamfara.