✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle ya rungumi kaddara kan faduwa zaben Gwamnan Zamfara

Matawalle ya sha kaye a hannun dan takarar jam'iyyar PDP, Dauda Lawal Dare.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya amsa shan kaye a zaben Gwamnan jihar da aka kammala tare kuma da neman afuwar al’ummar jihar.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare ne ya kayar da Gwamnan a zaben ranar Asabar.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wani sakon murya da ya fitar ga al’ummar jihar, inda ya ce shi da magoya bayansa sun karbi kaddara.

Ya ce, lokacin da gwamnatinsa ta karbi mulki, ya zauna tare da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar wajen ganin an samo hanyoyin dawo da zaman lafiya ta hanyar tattaunawar zaman lafiya.

Ya ce har zuwa yau, babu abin da ya fi addabar jihar kamar rashin tsaro da ake fama da shi.

Matawalle ya ce baya ga tattaunawar zaman lafiya da ’yan bindiga, ya kuma yi aiki tukuru wajen ganin gwamnatinsa ta kawo dukkan bangarorin siyasa karkashin inuwa daya don zaman lafiya da hadin-kai ya wanzu a fadin jihar.

Ya ce, sun samu nasarar sasanta bangarorin siyasa da ba sa ga maciji da juna, wanda kuma shi ya bude hanyar gudanar da yakin neman zabe a jihar lami lafiya ba tare da wata matsala ba.