✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawalle ya yi martani kan raba wa Sarakunan Zamfara motoci na alfarma

Motoci guda sha bakwai kacal muka raba ba 200 ba.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Jihar Zamfara ya mayar da martani kan cece-ku-cen da ya biyo bayan raba wa sarakunan gargajiya a jihar motoci da kuma alakantan sayen motocin da zunzurutun kudin da aka kiyasta cewa ya kai biliyoyin nairori.

Wasu ’yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu a game da batun raba motocin, inda suka nuna rashin gansuwa da lamarin, amma wasu suna ganin hakan a matsayin taimaka wa sarakunan ne sabili da rashin tsaro da suke yawan fuskanta.

Tun bayan da labarin raba motoci kirar Cardillac wanda aka kera a shekarar 2019 sama da 200 ga sarakunan gargajiya a Jihar Zamfara ya karade kafafen sada zumunta ne ‘yan Najeriya daga shiyoyin kasar daban-daban ciki har da Kudanci kasar suke tofa albarkacin bakinsu a game da lamarin.

Wasu ’yan kasar dai sun yi ta ba da misali ga labarin raba karin motoci ga cibiyar tsaro ta Yammacin Najeriya, wanda aka fi sani da suna Amotekun da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi a cikin watan Afrilu inda ake cewa ya ya za’a yi jihar dake fama da tarin matsalolin tsaro ta raba motoci masu tsada ga sarakuna.

A bayanin da ya yi wa Muryar Amurka, gwamna Bello Matawalle ya ce motoci guda goma sha bakwai ne ya raba ba 200 ba, sannan kuma sarakunan da aka bai wa motocin an tabbatar da cewa basa hulda da ‘yan ta’adda kuma suna da mukami da rikon gaskiya, kuma ba abu ne mai kyau ba ace sarakuna irin wadannan basu da motar hawa.

A game da tambayoyi da ’yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta suka yi ta yi na cewa shin gwamna Matawalle ya taba taimakon jami’an tsaro a jiharsa da kayan aiki, kwamishinan ‘yan sandan Jihar Zamfara, CP Ayuba El-Kana ya bayyana cewa gwamna Matawalle ya taimaka masu da motocin aiki kuma ya basu goyon baya wajen aikinsu da yaki da ‘yan ta’adda.

Aminiya ta ruwaito yadda gwamnan ya raba wa duk masu rike da masarautun gargajiya 260 motoci na alfarma a Jihar Zamfara.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya bude babbar hedikwatar Majalisar Malamai ta jihar a Yammacin ranar Larabar makon jiya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ne ya jagoranci rabon motocin wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

Sarkin Musulmin ya yaba wa Gwamna Matawalle dangane da yadda ya riki inganta jin dadin masarautun gargajiya da muhimmanci, wanda a cewarsa har yanzu su ne ginshikin hadin kan al’umma.

Ya yi kira ga Sarakunan gargajiyar da su ci gaba da bai wa Gwamna Matawalle goyon bayan da ya dace musamman a fafutikar da gwamnatinsa take yi na ganin ta kawo karshen kalubalen da al’umma ke fuskanta a jihar.

A nasa bangaren, Gwamna Matawalle ya ce wannan tagomashi na da madogara da yadda sarakunan gargajiyar suka zamanto wani tubali kuma jakadu na addini da al’ada wadanda ya ce su ne kashin bayan hadin kai da zaman lafiya na kowacce al’umma.

“A dalilin haka ne gwamnatina ta ke martaba sarakunan gargajiya da kuma masarautunsu.

“Wannan ya sa muka ga ya dace mu sayo musu sabbin motoci na alfarma don inganta walwala da jin dadinsu.

“Mun siya musu sabbin motoci samfurin Cadillac kirar 2019, wadanda za a raba wa Sarakuna 17, Iyayen Kasa 13 da kuma Dagatai 230 da ke fadin jiharmu,” a cewar gwamnan.