✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsafa sun kashe mutum 3 a Oyo

Ana kyautata zaton matsafa ne suka kashe mutanen.

Al’umar Karamar Akinyele da ke Jihar Oyo sun shiga zullumi sakamakon dawowar ta’addancin matsafa a yankinsu a ‘yan kwanakin nan.

A ranar Litinin ce dai aka tsinci gawarwaki uku wanda ake kyautata zaton aika-aikar matsafa ce ta hallaka su.

Daga cikin gawarwakin, an fille wa daya kai, yayin da aka cire wasu muhimman sassan jikin ragowar biyun.

Majiyarmu ta ce an gano duka gawargwakin ne a gefen babbar hanyar shiga Ibadan a yankin na Akinyele da safiyar Litinin.

Bayanai sun ce ana zargin an kashe mutanen ne ta hanyar makure musu wuya.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batu, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya ce ”Ana kan bincike, kuma duk halin da ake ciki za a sanar da al’umma.”

Sai da har zuwa lokacin hada wannan rahoton rundunar ba ta fitar da wata sabuwar sanarwa a kan batun ba.