✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsafa sun yi wa ’yar shekara 13 fyade

Wasu mutane da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun yi wa wata yarinya mai shekaru 13 fyade ayankin Igando da ke Legas. Fyaden da…

Wasu mutane da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun yi wa wata yarinya mai shekaru 13 fyade ayankin Igando da ke Legas.

Fyaden da aka yi mata a unguwar Igando na zuwa ne kasa da mako daya bayan Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Hakeem Odumusu ya sha alwashin kama wadanda suka yi wa wata mai shekara 13 fyade a unguwar Ejigbo, a jihar.

Mazauna sun yi ta Allah-wadai tare mamaye ofishin ’yan sanda yankin domin mika koke da kuma gira da a damko wadanda ke da hannu a lamarin.

Rahotanni sun nuna daya daga cikin wadanda ake zargin wanda ya gudu ne daga aji ukun karamar sakandare yanzu kuma yana sana’ar kanikanci.

Aminiya ta gano cewa zuwan baturen ’yan sandan yankin CSP Taiwo Kasumu a kan lokaci da tawagarsa ya taimaka sosai wajen kama jagoran gungun matsafan.

Majiyarmu ta ’yan sanda ta ce binciken na farko-farko ya gano daya daga cikin wadanda ake zargin ne ya kama musu dakin otal a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2020 domin aikata ta’asar.

A ranar Talata bayan mahaifiyarta ta fita daga gida daya daga cikin matasan ya je gidan ya yaudare ta zuwa dakin inda suka yi amfani da ita daya bayan daya har sai da ta fara zubar da jini.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton kokarinmu na jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Olumuyiwa Adejobi ya ci tura saboda bai daga wayarsa ko kuma masa rubutaccen sakon da aka tura masa ba.