✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar biyan kudin abubuwa a lokaci daya ta kau

Sirrin da masu kudi suka sani shi rashin biyan kudin abun da suka saya a lokaci guda

Wani sirri da masu kudi suka sani shi rashin biyan kudin abu a lokaci guda!

A shekarun bayan nan yawancin ’yan Najeriya sun shaida yadda faduwar darajar Naira ta haifar da tsadar rayuwa da tashin gwauron zabon farashin kaya.

Saboda haka yana da muhimmanci duk wani ma’aikaci a Najeriya ya kasance mai zurfafa tunani kan hanyoyin gudanar da kudade.

Mukan yi aiki tukuru mu samu kudi, kuma a matsayinmu na ’yan Najeriya muna son kayatattun abubuwa da kuma jin dadin rayuwa a lokacin da muke raye! Babu laifi yin hakan, domin sau daya tal ake rayuwa.

Amma abin tambaya shi ne: “Ta wace hanya za ka samu kyawawan abubuwan rayuwa, ka yi rayuwa daidai matsayinka tare da samun cigaba daidai da karfinka?”

Idan kai mazaunin daya daga cikin manyan biranen Najeriya ne, daga cikin manyan abubuwan da za ka fi kashe kudi a kai a shekara akwai biyan kudin haya.

Sau tari bayan mun biya kudin haya, mukan bukaci tallafin kudi ko rance, kasancewar kudin hayarmu kan kai kashi 30% na kudaden da muke samu a shekara.

Galibi bayan ka biya haya, kakan gagara biyan kudaden wasu muhimman abubuwa kamar kudin makaranta, kudin asibiti, kudin gyaran gida da sauransu – sai ka ji abubuwan sun yi maka yawa.

Ba a ma maganar sauran abubuwa kamar zuwa hutu, kyalliya da kawa da shakatawa – saboda haka sai ya kasance da ka gama biyan kudin wani abun, na gaba na jira.

Gaskiya kowannensu na da muhimmanci, amma idan babu nagartaccen tsari ko tallafi za ka takura.

Na dade ina jin dadin biyan kudin abubuwa da kadan-kadan.

Manyan masana harkar kudi da attajirai sun san haka, shi ya sa ba kasafai suke biyan kudin abun da suka saya a lokaci guda ba, musamman idan abun na da tsada.

Biyan kudin abubuwa da kadan-kadan zai ba ka damar samun abubuwa da yawa ba tare da ya takura ko ka ya yi fama da rashin kudi ba.

Muhimmiyar hanyar tafiyar da kudi ce da ya kamata a rika amfani da ita idan da hali.

Shi ya sa na gano PayWithSpecta nake kuma son shi, saboda hanya ce ta sayen abubuwan da kake bukata ta hanyar biyan wani kaso na kudinsa na tsawon lokaci.

PayWithSpecta

Yaya PayWithSpecta ke aiki? Idan ka bude asusun, PayWithSpecta za su rika biyan kudin duk abin da kake son saya, gwargwadon yawan kudinka a asusun.

Hakan zai ba da dama su biya dan kasuwar da ka yi sayayya a wurinsa kudinsa kacokan, kai kuma duk wata za a rika cirar kudin da kadan-kadan daga asusunka.

Damar jinkirta lokacin biyan kudin sayayya daya ne daga manyan ginshikan tsarin banki a duniya.

Yana ba da damar samun bunkasa da kuma kirkira saboda ba ka da damuwa cewa sai ka sayi abin da kake so kudi hannu.

Da PayWithSpecta kowa na iya sayen abubuwa ba tare da ya dakatar da sauran abubuwan ba.

Ina ganin PayWithSpecta a matsayi wata hanyar cimma burikanmu na kashin kai da kuma ta fuskar kwarewa.