✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar ruwan fanfo ta zo karshe a kauyukan Yobe

Kauyukan sun shafe shekaru suna amfani da gurbataccen ruwa.

Al’ummar wasu garuruwa a Karamar Hukumar Fika ta Jihar Yobe da suka shafe shekaru suna fama da matsalar tsaftataccen ruwan sha, sun wayi gari cikin murna suna diban ruwan a fanfo a ranar Litinin.

Garuruwan da suka hada da Ngeji da Gadaka da garin na Fika, sun samu ruwan ne a lokacin da Sanatan mai wakiltar Kudancin Yobe, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai, ya musu dalilin ta hanyar kai kokensu gaban Majalisar Zartarwa ta Kasa.

Majalisar Zartarwa ta amince da a samar da ruwan shan a yankunan karkarar da suka share shekara da shekaru suna rayuwa babu ruwan sha.

Aikin ya samar wa wadannan yankunan karkara tsaftataccen ruwan sha a karon farko, wanda kuma zai taimaka musu wajen ayyukansu na yau da kullum.

Hakan zai kuma zai kare su daga shan gurbataccen ruwa da ke haddasa cutar kwalara da dai sauransu.

Dattawan yankunan da suka samu ruwan sun yi alkawarin kula da aikin saboda amfaninsu, tare da godiya ga Shugaba Buhari da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni da Sanata Ibrahim Bomai da ya kai kokensu da kuma Sarkin Fika Muhammad Ibn Abali, bisa wannan aikin alkhairi.

Wani mazaunin garin Fika da muka zanta da shi, Madu Ibrahim, ya ce, “Tsawon shekaru masu yawa yankunan karkarar suna kukan rashin wadataccen ruwan sha mai tsafta a tsakanin yankunan nasu amma yanzu wannan matsalar ta zama tarihi a gare su.

A cewarsa, ruwa shi ne komai a rayuwa kuma jigon cigaban al’umma wanda ba a iya kayyade amfaninsa a rayuwar dan Adam.