✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: A kafa dokar ta-baci a Arewa —Matawalle

Gwamnan ya nuna damuwa matuka kan yadda ake kai hare-hare a yankin.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya yi kira da a sanya dokar ta-baci a duk Jihohin Arewacin kasar dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin.

Sasshen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin wata tattaunawa da ya yi da mataimakin shugaban ’yan sanda da ke lura da shiyya ta 10 da ke Gusau, Ali Janga.

Gwamnan, wanda ya nuna damuwa matuka kan yadda ake kai hare-hare a mafi yawan jihohin yankin, ya yi amannar cewa sanya dokar ta-bacin za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron.

Yankin arewacin Najeriya ya hadar da shiyoyi uku, shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya ga kuma Babban Birnin Kasar na Abuja da ke yankin.

Shekaru masu yawa, yankin ke fama da ayyukan ’yan tada kayar baya da suka hada sace mutane don neman kudin fansa da tashe-tashen bam, da harin ’yan fashin daji da dai sauransu.

Kuma kafin yanzu an kashe daruruwan mutane a yankin yayin da irin wadannan rikice-rikice suka tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

Kungiyar Boko Haram da ISWAP sune suka fi damun yankin Arewa maso Gabas, yayin da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma ’yan fashin daji su ka fi addabar yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.