✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Gazawa ce kafa dokar ta baci a Anambra

PDP ta ce kafa dokar ta baci alamar gazawar Gwamnatin Tarayya ce.

A yayin da Gwamnatin Tarayya ke barazanar saka dokar ta baci a Jihar Anambra saboda tabarbarewar tsaro a jihar, jam’iyyar PDP ta bayyanawa yunkurin a matsayin tabbacin gazawar gwamnatin.

A nashi bangaren, tsohon Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Ambrose Aisabo, ya ce muddin aka dage zaben gwamna da ke tafe a jihar da sunan matsalar tsaro, to ya zama wajibi a sallami manyan shugabannin tsaron kasar daga bakin aiki.

Hakan na zuwa ne bayan Kwamishinan Yada Labaran Jihar Anambra, Mista C. Don Adinuba, ya nasar da yunkurin sanya dokar ta ta baci, a ranar Laraba, saboda karuwar hare-haren haramtacciyar kungiyar IPOB, wadanda ke lakume rayuka da dukiyoyin jama’a.

Tun da farko, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya sanar da hakan, yana mai nuni ga yadda hare-haren ke ci gaba da karuwa, a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Malami ya ce gwamnati za ta dauki matakan da suka dace wajen ganin an tabbatar da dimokuradiya a jihar da kuma gudanar da zabe.

Ministan ya kara da cewa, muddin aka samu barazana ga zaman lafiyar kasa da kuma karan tsaye ga dokokin dimokuradiya, babu tantama za su dauki matakan da suka dace, ciki har da saka dokar ta baci.

Ya ce hakkin gwamnati ne na tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa tare da kare dukiyoyin al’umma, sannan matsayinsu a gwamnatance shi ne za a ci gaba da shirin gudanar da zabe kuma za su samar da tsaron da ya dace.

Ita ma da take tsokace game da kalaman minsitan, kungiyar al’ummar yankin Yarabawa, ta bukaci daukacin shugabannin yankin Kudu maso Gabas da su yi wa tufkar matsalar hanci.

Sun ce ba sa goyon bayan sanya dokar ta baci a jihar, wanda alama ce ta gazawar gwamnati, amma duk da haka, wajibi ne shugabanni da iyayen yankin su san hanyoyin da za su tattauna da mutanensu, musamman matasansu domin yayyafa wa wutar fitinar wuta.

IPOB dai ta dade tana tursasa wa mutane zaman gida gami da kai musu hare-hare a sassan Kudu maso Gabas.

Duk da cewa a baya hare-haren sun fi kamari a Jihar Imo, a baya-bayan nan lamarin ya kara kazancewa a Jihar Anambra inda ake shirin gudanar da zaben gwamna a rana 6 ga watan Nuwamba.