✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Matsalar tsaro: An kafa gidan rediyon ‘yan sanda a Najeriya

An bude gidan rediyon ne don kyautata alaka tsakanin 'yan sanda da jama'a.

A ranar Laraba ne Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi bikin bude sabon gidan rediyo don kyautata alaka tsakaninta da jama’a.

Babban Sufeton ‘yan sanda Najeriya, Mohammed Adamu ne ya jagoranci bikin bude gidan rediyon mai suna ‘Nigeria Police 99.1FM’ a birnin Abuja.

“An bude wannan gidan rediyon ne don kyautata alaka tsakanin jama’a, tare da taimakawa wajen rage aikata laifuka.

“Za a rika yada labarai game da yadda za a kama masu aikata laifuka,” a cewar Adamu.

Tuni gidan rediyon ya kama aiki bayan samun sahalewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).

Babban sufeton ‘yan sandan ya kara da cewa, gidan rediyon zai rika gabatar da shiri na kai-tsaye ga ‘yan Najeriya, ta yadda za su rika kiran waya suna shigar da rahoto game da  yanayin tsaro a yankunansu.

Ya ce hakan zai inganta ayyukansu ta yadda za su gano masu aikata laifuka da zarar an shigar da rahoto da kuma kai wa jama’a dauki cikin gaggawa.