✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar Tsaro: An takaita zirga-zirgar Keke NAPEP a Lokoja

Shugaban karamar hukumar ya sanya dokar saboda matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.

Shugaban Karamar Hukumar Lokoja a Jihar Kogi, Muhammad Dan’Asabe Muhammad, ya sanya dokar hana zirga-zirgar babur mai kafa uku a fadin garin Lokoja bayan karfe 10:00 na dare. 

Don haka ya bayar da umarnin a kama duk wani direban babur din da aka kama ya karya dokar.

Muhammad ya ba da umarnin ne a ranar Litinin yayin wani taron tsaro na musamman a Lokoja, inda ya bayyana cewa haramcin ya zama dole saboda yawaitar aikata laifuka a garin.

Ya kuma bai wa mazauna garin tabbacin jajircewar gwamnatinsa na tabbatar da tsaro a kowane lokaci domin bunkasa tattalin arzikinsu da cigaba.

Har ila yau, shugaban karamar hukumar ya bukaci jami’an tsaro da su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawar da kungiyoyin asiri da sauran laifuffukan da ke faruwa a karamar hukumar, wadanda ke haifar da rashin kwanciyar hankali a ’yan kwanakin nan.

Shugaban karamar hukumar wanda ya kaddamar da rigunan tantance masu sana’ar babura a karamar hukumar, ya bukaci shugabannin kungiyoyin biyu da su bi umarnin dokar da aka kafa.

Sai dai ya yi gargadin cewa saba wa dokar zai haifar da tsattsauran hukunci ga wanda aka kama da laifi.