✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro ba ta damu manyan Arewa ba —#SecureNorth

#SecureNorth ta zargi shugabannin Arewa da kin ba da muhimmnacin ga matsalar tsaron yankin.

Matasan Arewa sun caccaki jagororin yankin kan yadda suka mayar da hankali kan zanga-zangar #EndSARS fiye da matsalar tsaro da ke barazana ga yankin.

Matasan masu zanga-zangar #SecureNorth mai rajin ganin an samar da tsaro a Arewa sun kalubalanci shugabannin yankin cewa sai yaushe za su dauki mataki a kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.

“Kun yi zama ranar 3 ga Nuwamba, 2020 inda kuka tattauna a kan zanga-zangar #EndSARS da matsalar shafukan sadar da zumunta; To sai yaushe za ku fara aiki a kan matsalolin tsaron da ke ci wa jama’arku tuwo a kwarya?

“Talauci, rashin ilimi da shan kwayoyi na neman kassara daukacin yankin Arewa, amma bututuwa 13 daga cikin 18 na cikin takardar bayan taronku sun karkata ne a kan zanga-zangar #EndSARS.

“Kun zabi ko boye hakikalin matsalar da ke addabar Arewa wanda kuka dunkule cikin jimla daya a cikin sakin layi na 11; Ba za mu lamunta ba.

“Saboda haka muna kiran dukkanninku ku tashi tsaye ku sauke nauyin da ya rataya a kanku; Dole ku tunkari ainihin matsalar yankin ku kuma mangance ta”, inji budaddiyar wasikar kungiyar ta #SecureNoth ga shugabannin Arewa.