✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Birtaniya ta horas da dakaru 145 a Najeriya

Muna fatan ganin wannan aiki ya dore domin samar da ingantaccen tsaro a kasar.

Rundunar Sojin Saman Najeriya tare da hadin guiwar Sashen Horas da Jami’an tsaro na Birtaniya, sun horas da dakarun soji 145 da za su yaki matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar nan.

Daga cikin jami’ai 285 da aka tantance, guda 150 ne kawai aka samu sun cancanta kuma a karshe dai 145 daga cikinsu ne kacal su kai nasara a darussan daukar horon.

Da yake jawabi a bikin yaye daliban da aka gudanar a cibiyar bayar da horo ta Rundunar Sojin Sama ta Kasa da ke Bauchi, Babban Hafsan Sojin Sama na kasa, Air Marshal Oladayo Amao ya bayyana yakinin da yake da shi na cewa jami’an sun samu horon da ya dace domin gudanar da ayyuka na musamman da za su kai ga cimma nasarar kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.

Amao wanda Babban Hafsan da ke kula da sashin tsare-tsare na rundunar, Air Vice Marshal Charles Ohwo ya wakilta, ya kuma ce a ci gaba da yunkurinsa na ganin an inganta da dorar da ingantaccen ayyuka, yanzu haka rundunar ta horar da jami’ai dubu biyar da kuma wasu na musamman dubu biyu.

A nasa bangaren shugaban sashin horaswa na sojin Birtaniya, Kanal Rory Shannon ya alakanta wannan nasara da aka samu a matsayin wadda ta samo asali daga kawance mai karfi da ke tsakanin kasashen biyu.