✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Buhari ya nemi taimakon sojin Amurka

Buhari ya bukaci Amurka ta dawo da hedikwatar rundunar AFRICOM zuwa Afirka

Shugaba Buhari ya bukaci taimakon Amurka wurin yaki da ayyukan ta’addanci don dakile bazuwarsu a Najeriya da sauran kasashen Afirka. 

Buhari ya mika kokon baran ne a yayin tattaunawarsa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, ta bidiyo a ranar Talata.

“Taimakon manyan kawaye irin Amurka muhimmi ne, duba da yadda illar rashin tsaron za ta shafi kasashen (yankin); shi ya sa hadin kan ke da muhimmanci wajen shawo kan matsalar,” inji shi.

Ya ce, “Matsalar tsaron Najeriya babbar abar damuwa ce a gare mu, ganin yadda tasirinta ya karu saboda sarkakiyar sha’anin tsaro a yankin Sahel da Yammacin Afirka da kuma Yankin Tabkin Chadi.

Ko da yake bai fayyace taimakon da kasashen Afikra suke bukata ba, Buhari ya bukaci Amurka ta dauke sansanin rundunarta ta musamman kan Afirka (AFRICOM) daga kasar Jamus ta dawo da shi Afirka, idna za ta gudanar da ayyukanta na karfafa sha’anin tsaro a nahiyar.

Ya bayyana hakan ne a yayin da matsalolin tsaro suka dabaibaye Najeriya, ta yadda ake ganin bukatar kasar ta nemi taimakon kasashen waje, saboda bisa alama matsalar na neman gagarar dakarun kasar.

Ta’addanci, yunkurin ballewa daga Najeriya, satar mutane, da sauransu su yi wa kasar tarnaki tare da sanadiyyar mutuwa daruruwan mutane a baya-bayan nan.

A cewar Buhari, “Matsalar tsaron Najeriya babbar abar damuwa ce a gare mu, duba da yadda tasirinta ya karu sakamakon sarkakiyar sha’anin tsaro a yankin Sahel da Yammacin Afirka da kuma Yankin Tabkin Chadi.

“Karuwar barazanar tsaro a Yammaci da Tsakiyar Afirka, Tekun Guni, Tabkin Chadi da yankin Sahel, da kuma tasirin hakan ga nahiyar Afirka, ya jaddada muhimmancin dawo da matsugunin rundunar AFRICOM daga Stuttgart na kasar Jamus zuwa wurin aikinta a nahiyar Afirka,’’ inji sanarwar da kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya fitar.

Buhari ya kuma yaba wa Gwamnatin Shugaba Joe Biden na Amurka bisa soke dokar da ta sanya takunkumi ga baki masu ziyartar Amukra da daga kasashen Musulmai.