✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Dalilin da muka tuhumi Waziri kan kalamansa – Masarautar Katsina

Masarautar ta ce ba don ta tozarta shi ba ta tuhumi kalaman nasa.

Masarautar Katsina ta yi karin haske a kan tuhumar da ta yi wa tsohon Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga kan wasu kalamansa a kan matsalar tsaro a jihar, wace har ta yi awon gaba da rawaninsa.

Sai dai masarautar ta ce ba don ta tozarta shi ta aike masa da tuhumar ba, sai don ya yi karin haske a kalaman da ya yi, saboda yadda ta ce yana da kima a idonta.

Farfesa Sani dai yayin wani taron manema labarai a birnin Ilorin na Jihar Kwara, ya yi tsokaci a kan matsalar tsaron ta ki cit a ki cinyewa a Jihar, kalaman da bisa ga alama ba su yi wa masarautar dadi ba.

Yayin zantawarsa da Sashen Hausa na BBC ranar Juma’a, Sakataren masarautar, kuma Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo, ya ce masarautar na neman karin haske ne daga Wazirin kan kalaman nasa, la’akari da kimarsa.

Sakataren ya kuma ce bai kamata mai rike da matsayi irin nasa ya rika sakin baki yana maganganu irin wadancan ba musamman kan sha’anin tsaro.

A cewarsa, masarautar ta yi matukar mamakin yadda a maimakon ya mayar da amsar tuhumar, sai ya bige da yin murabus.

Idan za a iya tunawa, masarautar ta Katsina a wasikar tuhumar da ta aike wa Farfesa Lugga ta zarge shi da yin wasu kamalai ne a wata jihar da take gani basu kamata ba.

A cikin bayanin Wazirin mai murabus, ya ce matsalar ta shafi wasu Kananan Hukumomi, bayan rufe wasu makarantu har ta kai ga tilasta wa wasu Dagattai da Hakiman masarautar yin hijira.