✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Fintiri ya hana hawa babura a kananan hukumomi 2

Gwamnatin jihar ta ce ba sani ba sabo ga duk wanda ya karya dokar.

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri ya sanya dokar takaita zirga-zirgar babura a kananan hukumomin Yola da Girei daga karfe 5 na yamma zuwa 5 na asuba.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar a yammacin ranar Talata.

Sanarwar ta ce, “Dokar takaita zirga-zirgar babura ta fara aike a ranar Talata 8 ga Fabrairu 2022, nan take.”

Gwamnatin Adamawa ta ce ta sanya sabuwar dokar duba da yadda ayyukan bata-gari ke ci gaba da kamari wajen kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Sai dai Gwamna Fintiri, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar duk wanda ke son hana tabbatuwar zaman lafiya a jihar.

“Suna neman zama barazana ga zaman lafiya, tsaro, ci gaban al’umma da tattalin arziki, don haka dole a dauki matakin gaggawa a kansu.”

Ya ce babu wata gwamnati da za ta bar al’ummarta cikin fargaba game da sha’anin tsaronsu, kuma dole ce ta sa ta yanke hukunci don yakar fashi da makami, sace-sace da sauran miyagun laifuka a kananan hukumomin Girei da Yola.

Kazalika, dokar ta tanadi hukuncin daurin wata shida ko tarar kudi N100,000 kuma babu sani ba sabo ga duk wanda aka samu ya karya dokar.

Sai dai gwamnatin ta ce wadanda ke da wani uzuri da ya shafi bukatar gaggawa kamar sha’anin lafiya da sauransu za a iya daga kafa, inda bukatar hakan ta taso.

Gwamnatin ta ba wa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro damar cafke tare da gurfanar da duk wanda ya karya sabuwar dokar.