✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara ta dauke sansanin NYSC daga Tsafe

An sauya wa sansanin matsuguni sakamakon matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin Zamfara ta sauya wa sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) matsuguni daga Karamar Hukumar Tsafe zuwa Gusau, babban birnin jihar sakamakon matsalar tsaro.

Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha, shi ne ya sanar da haka a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Hukumar NYSC Birgediya-Janar M K Fadah.

A bayankinsa kan yanayin tsaro a jihar, Sanata Nasiha ya shaida wa shugaban hukumar cewa a hankali ana samun kwanciyar hankali, jama’a na ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a jihar.

Har wa yau, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi magana da hukumar NYSC kan dakatar da ayyukan sansanin a jihar sakamakon kalubalen tsaro da ya ta’azzara.

Ya bayyana takaicinsa kan koma bayan da aka samu, lamarin da ya sa gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ya bayar da umarnin a sauya wa sansanin nan NYSC matsuguni na wucin gadi don ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar sauran jiha.

Mataimakin gwamnan, ya taya Birgediya-Janar M K Fadah murnar nadin da aka yi mishi a matsayin Darakta-Janar na NYSC, ya kuma tabbatar mishi da kudirin gwamnatin jihar na samar da duk abin da ake bukata domin daukar nauyin sansanin na NYSC na wucin gadi.

Da yake jawabi, Birgediya-Janar M K Fadah ya ce sun je jihar ne domin duba wurin da aka samar na wucin gadi da kuma zabar wuri mafi dacewa kamar yadda gwamnatin jihar ta amince.

M K Fadah ya ce da hukumar ta ji dadi kan yadda gwamnatin jihar take nuna damuwa game da sha’anin tsaro.

A cewarsa, kalubalen tsaro a yanzu ya zama ruwan dare a kusan kowace kasa, ciki har da Najeriya.