✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: JNI ta bukaci Musulmi su dukufa addu’o’i na musamman

Kungiyar ta bukaci masallatai, makarantu da majalisu su dukufa Alkunut.

Sakamakon damuwa da matsalolin tsaron da suka dabaibaye Najeriya, kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi kira ga Musulman Najeriya da su dukufa addu’o’i na musamman don nemna taimakon Allah.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren kungiyar, Dokta Khalid Aliyu ya fitar ranar Lahadi, JNI ta ce addu’a ita ce babban makamin mumini, kuma hanya daya tilo da za a iya bi a yanzu wajen neman dauki daga Ubangiji.

Sanarwar ta ce, “Allah madaukakin Sarki shi ne mai rahama mai jinkai, yana bukatar a koma gasheShi in aka shiga halin tsanani da kunci, saboda babu abin da ya fi karfinSa.

“Ga Musulmai, addu’a wata babban makami ce a dukkan halin da muka tsinci kanmu a rayuwa, amma sai dai abin takaici a Najeriya, yanzu mun tsinci kanmu cikin yanayin yawan aikata sabo, cin hanci da rashawa da kuma aikata barna,”

JNI ta kuma ce komawa ga Allah a yanzu ita ce kadai hanyar da ta rage wa Musulman Najeriya, ksancewar Allah ba Ya rufe kofar karbar tuba.

Sanarwar ta ce Shugaban kungiyar, kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga Musulman Najeriya da su fara yin Alkunut a karshen kowacce sallar farilla da ta nafila daga yanzu.

Kungiyar dai ta ce kiran ya zama wajibi la’akari da yadda ake ci gaba da kisan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba a sassa daban-daban na kasar nan.

Kazalika, JNI ta bukaci a limamai da majalisun karatun addini da makarantun Allo da na Islamiyya da dukkan kungiyoyin addini da su fara yin addu’o’i na musamman ga Najeriya, musamman yankin Arewa.