✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Matsalar tsaro: Ku kare kanku —kungiyar Kiristoci

Kungiyar ta ce dole ne a kawo karshen zubar da jinin da ake.

Kungiyar Matasan Kiristocin Najeriya (YOWICAN), ta yi kira ga ’yan Najeriya su tashi su kare kansu daga hare-haren maharan da ke yin kisan gilla a fadin kasar.

Shugaban kungiyar ta YOWICAN na Kasa, Belusochukwu Enwere, ne  ya yi kiran a Abuja, yana mai bayyana damuwa kan karuwar matsalar tsaro a Jihar Filato da wasu sassan Najeriya.

A cewarsa, yadda ake zubar da jinin wadanda ba su ji ba, ba su gani ba da cewa abun damuwa ne kuma abun Allah wadai.

“Na yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa sama da mutum 35 a Filato musamman Kiristoci a ranar 25 ga Agusta, 2021 cikin dare tare da kone coci-coci da Makarantar Kunga a kauyen Yelwan Zangam.

“Ba za mu lamunci wannan ba duk da cewa akwai bambanci kabila, addini da kuma bangaranci. Ina shugabanninmu suke?

“Tabon wannan kashe-kashe ba zai taba gushewa a zukatanmu ba. Yau a Filato wani a Kaduna, Binuwai da sauransu.

“Ya kamata ’yan Najeriya mu tashi mu kare kanmu kafin a karar da mu, sa’annan mu zauna lafiya da juna a matsayin ’yan kasa daya al’umma daya.

“Ina kira ga Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya da gwamnonin jihohi da jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayukan al’umma,” cewar Enwere.

Kazalika, kungiyar ta jajanta wa wadanda aka kashe wa ’yan uwa a baya-bayan nan a rikice-rikicen na Jihar Filato.