✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Ortom ya kalubalanci Buhari zuwa mahawara

Ya ce ya kamata Buhari ya magance matsalar ba ya tura ’yan baranda su kare shi ba.

Gwamna Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya kalubanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zuwa muhawara kan matsalar tsaro da ta yi wa Najeriya katutu.

A cewar Ortom, kamata ya yi Buhari ya mayar da hankali wajen kawo karsen kashe-kashe a Najeriya, ba tura ’yan baranda su caccke shi saboda ya tsage wa Gwamnati Buharin gaskiya ba.

“Har yanzu ina kan bakata game da abin da na fada a gidan talabijin na Channels, ina kuma kalubalantar su, su fito a mu yi muhawara a kan wannan batu a gidan talabijin din. Ba wanda zai yi min barazana,” inji shi.

Gwamnan ya bayyana wa ’yan jarida haka ne a Makurdi, babban binrin Jihar Binuwai, a martaninsa ga raddin da Fadar Shugaban Kasa ta yi masa kan hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

A cewarsa, martanin na Fadar Shugaban Kasa ba komai ba ne face kame-kame, kuma babu wata maganar dauka a ciki.

Sanarwar da gwamnan ya fitar ta hannun kakakinsa, Terver Akase, ta ce martanin da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, sun nuna irin Shugabancin Kasar da muke da shi a halin yanzu.

“Sun kau da kai daga sakon suna sukar mai maganar. Siffanta mutumin da ya rike muhimman mukamai a gwamnatin jiha da ta tarayya a matsayin ‘mara dattaku’, ya nuna cewa wadanda suka tsara wannan sako ba sa cikin hayyacinsu.

A cewar Ortom, mukaman siyasa da ya rike a baya, ciki har da minista da matsayinsa na gwamna a yanzu, sun tabbatar cewa shi yana da dattaku a siyasance.

“Shawararmu ita ce Fadar Shugaban Kasa ta kawo karshen kashe-kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, ta gyara tattalin arziki kamar yadda ta yi alkawari sannan ta kawar da rashawa da ake yi a karkashin mulkinta.

“Ba za su kauce wa nauyin da ya rataya a wuyansu ba. An zabe su ne domin su hidimta wa mutane ba wai su ci zalinsu ba, su danne musu hakkinsu na fadar albarkacin baki.

“Sanin kowa ne cewa sun yi alkawari a 2015 cewa za su kare, su kuma mutunta hakkokin ’yan Najeriya idan aka zabe su, amma abin takaici, yanzu akasin hakan suke yi wa ’ya Najeriya,” .

– Borin kunya Ortom ke yi —Kawu

Amma a wani raddi, tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dokoki, Abdulrahman Kawu, ya bukaci Ortom da ya daina dora laifin gazawarsa a matsayin gwamna a kan Shugaban Kasa.

Abdulrahman Kawu, wanda tsohon Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Sumaila-Takai ne, ya zargi Ortom da caccakar Shugaban Kasa ne domin kawar da hankalin mutane daga gazawarsa a matsayinsa na gawamna.

Ya kalubalanci gwamnan ya bayyana matakan da ya dauka domin magance matsalar tsaro a jiharsa, ko manyan ayyuka 10 da ya kammala ko yake kan yi a Jihar Binuwai.

Ya ce, “Ba wanda bai damu ba da matsalar tsaro da ta addabi kasar nan, amma dole a yaba kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na shawo kan matsalar a wuraren da abin ya shafa.

“Na yi mamakin karanta abin da Ortom ya fada a kan shugaban kasa, kuma ina ganin lokaci ya yi da ya kamata mutane su yi watsi da ’yan siyasa irinsa masu fakewa da siyasa domin boye gazawarsu.

“Dole mu fito mu fallasa ’yan siyasa irinsa domin mutane su gane su,” inji shi.

Daga Sagir Kano Saleh da Hope Adama Emmanuel (Makurdi) da Ibrahim Giginyu (Kano).