✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Rarara ya shirya taron addu’a na musamman ga Najeriya

Mawakin ya shirya taron addu'a don samun zaman lafiya a Najeriya.

Shahararren mawakin nan na Buhari, Dauda Kahutu Rarara, ya shirya taron addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Daruruwan mawaka da jaruman Kannywood ne suka halarci taron addu’ar ta musamman da kungiyar 13X13 ta shirya a Kano.

Kungiyar da aka kafa don bunkasa ayyukan masana’antar fim, Rarara ne ke jagorantar ta a matsayin shugabanta na kasa.

Da yake jawabi bayan kammala zaman addu’ar, Rarara ya ce taron addu’ar ba shi da wata nasaba da siyasa, baya ga neman taimakon Allah domin a samu zaman lafiya da hadin kai a tsakanin al’umma.

“Hukumomin tsaro, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dawo da zaman lafiya a wannan kasa mai albarka. Haka nan masana’antar fim ta Arewa da sauran yankuna

“Abin da Najeriya ke bukata shi ne addu’a, shi ya sa muka shirya wannan taro na musamman na addu’a tare da masu ruwa da tsaki a harkar nishadantarwa na Arewa domin yi wa Najeriya addu’ar zaman lafiya da hadin kai.

“A fili yake idan babu zaman lafiya babu abin da zai motsa kamar yadda ake tsammani,” in ji Rarara.

An gudanar da karatun Al-kur’ani na musamman tare da yanka rakuma biyu a lokacin addu’ar ta musamman da mawaka da jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa da dama suka halarta.