✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Secondus ya bukaci Buhari ya yi murabus

"Buhari ya gaza babu wani sauran uzuri da za a masa, dan haka ya yi murabus," cewar Secondus.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus sanadiyar kalaman da ya yi a kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Secondus ya yi wannan martani ne a ranar Asabar ta hannun mai ba shi shawara a kan kafafen watsa labarai, Mista Ike Abonyi.

Furucin da Shugaban Kasar ya yi a ranar Alhamis na cewa katabus din da jami’an tsaro ke yi bai wadata ba wajen magance ayyukan ta’addaci a kasar nan shi ne ya fusata Shugaban na PDP.

“Na yi mamakin kalaman Buhari, duk da irin kiraye-kirayen da aka rika masa a kan ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar nan, amma ya yi kunnen uwar shegu da mutane, sai kuma a yanzu zai ce sun gaza.

“A matsayinsa na Shugaban kasa, kuma Kwamandan tsaro, ya kamata ya daina kame-kame ya amsa cewa ya gaza,” in ji Secondus.

Ya kara da cewa kalaman na Buhari ba komai ba ne, face gazawa da kasa shawo kan matsalar tsaro, dan haka babu sauran wani uzuri da za a masa face ya yi murabus.