✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro ta hana Firaiminista kai ziyara a Mali

Firaiministan Mali, Choguel Kokalla Maiga ya dakatar da ziyarar sa a yankin Arewacin kasar sakamakon barazanar matsalolin tsaro. Maiga mai shekaru 64 ya isa birnin…

Firaiministan Mali, Choguel Kokalla Maiga ya dakatar da ziyarar sa a yankin Arewacin kasar sakamakon barazanar matsalolin tsaro.

Maiga mai shekaru 64 ya isa birnin Gao a ranar Juma’ar da ta gabata a ziyarar aiki ta kwanaki 4, yayin da cikin ziyarar aka tsara zai ziyarci garuruwan Bourem da Ansongo.

A yanzu dai an dakatar da ziyarar garuruwan biyu, saboda rahotannin ta’azzarar hare-haren ‘yan ta’adda, kamar yadda guda daga cikin kusoshin gwamnatin kasar ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

Magajin garin, Bourem Hamadou Mahammane Toure, ya tabbatarwa da manema labarai soke ziyarar, wadda ke zama karon farko da firaiministan ya kai Arewacin kasar tun watan Disamba, bayan fama da cutar shanyewar barin jiki.

A yayin ziyarar dai an shirya Maiga zai tattauna da shugabannin al’umma da sojojin da ke bakin daga.

Haka kuma, an tsara zai raba wa manoma kayayyakin aikin gona da nufin rage musu radadin ayyukan ta’addancin, yayin da zai kaddamar da wasu ayyukan ci gaba a yankunan, wadanda gwamnati ta samar.