✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro ta takure tattalin arzikinmu —Buhari

Buhari ya jinjina wa hukumomin tsaron Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta na ci gaba da takure asusun gwamnati da albarkatun kasa wajen magance ta.

Buhari ya ce matsalar tsaron na barazanar gurgunta shirin aike da jami’an tsaro da albarkatun kasa da kuma yanayin tsaro a kasar.

Ya bayyana haka ne ranar Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da wani daftari na takaita rikice-rikice ta kasa da nufin cike gibin da aka samu ta hanyar aike da jami’an tsaro masu yawa ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Shirin da ofishin mai bai wa shugaban shawara kan harkar tsaro da kuma hadin gwuiwa da hukumomi, zai tabbatar da cewa an samu nasara wajen dakile rikice-rikice a fadin kasar.

Buhari ya tuna cewa a lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, Najeriya na fuskantar matsalolin rashin tsaro da dama kama daga ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da satar danyen mai da sauransu.

Har ila yau, shugaba Buhari ya jinjina wa mai taimaka masa a bangaren sha’anin tsaro da kuma sauran hukumomi saboda samar da shirin, inda ya ce hakan ya nuna zimmar da ake da ita na ganin an magance rikice-rikce a fadin kasar.