✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro ta tilasta wa manoman Kaduna yin noma a gefen hanyoyi

Hakan na faruwa ne saboda kalubalen tsaro

Hare-haren ’yan bindiga sun tilasta wa manoman Kaduna da dama barin gonakinsu da ke cikin dazuka zuwa gefen gari ko kan hanyar a tsakanin Kaduna zuwa Zariya.

A lokuta da dama akwai bayanai kan yadda ’yan ta’addan ke sacewa tare da kashe manoma a gonakinsu ko a hanyarsu ta zuwa gona a kauyukan kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chikun da Kajuru da Kagarko wadanda suke fama da matsalar tsaro.

A yanzu duk matafiyi a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya zai ga manoma sun dawo gefen hanya da noma domin samun kwanciyar hankali.

Aminiya ta gana wa da wadansu daga cikin manoman da matsalar tsaro ta tilasta masu barin gonakinsu ciki har da Malam Jafaru Abdullahi mazaunin garin Unguwar Salahu da ke karamar Hukumar Giwa wanda ya gudu ya bar gonakinsa da suka kai 12 a cikin daji.

Malam Jafaru ya ce, a shekarun baya yana shuka kusan buhu 300 na masara da shinkafa da waken suya duk shekara, amma tilas ta sa ya bar kauyensu zuwa kauyen Gwada a karamar Hukumar Giwa.

Ya ce, duk da haka ’yan ta’addan sun ci gaba da matsa masu lamba lamarin da ya sa ya sake yin kaura zuwa kusa da wani kauye da ke Zariya da yin noma.

“Yanzu haka ina kusa da wani kauye a yankin Zariya ina noma, wannan shi ne halin da manoma a karkara ke ciki musamman wadanda suka fito daga kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro,” inji shi.

Ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda gwamnati ta kasa kare rayukan manoman karkara daga hare-haren ’yan ta’addan.

Ya ce, takaita noma a gefen gari ko bakin hanya zai janyo karancin abinci kuma hakan zai iya janyo yunwa a kasar nan.

Sarkin Kasuwar Rigachikun, Malam Salisu Manaja wanda wakilinmu ya tarar a gonarsa a gefen hanyar Kaduna zuwa Zariya ya nuna rashin jin dadinsu a kan yadda noma ya dawo gefen gari.

“Ba mu jin dadin hakan ba, amma dole ya sa mu barin gonakinmu da ke daji. Ko a nan din ma muna cikin tsaro domin da mun hango bakon ido mun rika waige-waige ke nan,” inji shi.

Ya kara da cewa, gaskiya idan ba a dauki mataki ba akwai yiwuwar a fuskanci karancin abinci a jihar domin ko a yanzu an hana su shuka masara ko dawa a gefen hanya saboda gudun samar da maboya ga miyagu.

Shi ma Bulus Ayuba manomi ne daga kauyen Kafin Gwari a Igabi kusa da garin Rigachikun wanda yake noma shinkafa a gefen hanyar Kaduna zuwa Zariya bayan ya baro gonarsa a cikin daji.

“A shekarun baya ina shuka masara da dawa da sauransu, amma a wannan gonar shinkafa kurum nake nomawa a nan gefen hanya, saboda ba za mu iya shiga daji ba. Hakan ya sa nake jin kewar gonata da ke cikin daji domin tana da girma kuma za ka iya shuka duk abin da kake so,” inji shi.

Ya ce, mutumin da ke shuka sama da buhu 10 na masara yanzu da kyar yake girbe buhu biyar hakan alama ce ta matsala. Wani manomi a kauyen Maigiginya a yankin Rigasa a Igabi, Malam Ridwan ya ce shi ma tuni ya daina zuwa gonarsa da ke daji saboda tsoron abin da ka iya faruwa.

Ya kara da cewa, akasarin manoman da ke kauyen sun yiwo kaura zuwa kusa da shingen jami’an tsaro da ke gefen garin.

Su kuma jami’an tsaron sun hana shuka duk wani abu da zai yi tsawo saboda gudun bai wa barayin mafaka.

Ya lissafo kauyukan da ya ce, duk sun watse kamar Maguzawa da Kwate da Beri-beri da Doka da Unguwar Malam da Kwate Waziri duk a yammacin garin Rigasa.

“Akasarin mutanen manoma ne kuma babu wata sana’a da suka iya da ta wuce noma, amma duk sun baro sun dawo cikin Rigasa, inda ake da karancin filin noma na haya ballantana su yi noman,” inji shi.

Noma a gefen hanya zai yi illa ga noman kasuwanci – Masana

Wani masanin noma kuma mai noman kasuwanci, Abdurrahman Ali Musa Tudun Wada ya bayyana cewa, sun dade suna fada wa gwamnatin hadarin da ke tattare da yin noma a gefen gari, amma ba a dauki mataki ba har ga shi abin ya fara zaman ruwan dare har a gefen hanyar mota.

Ya ce, a yanzu akwai gonaki da yawan gaske da aka yi watsi da su a cikin daji saboda masu su ba sa iya zuwa saboda tsoro.

Ya ce, muddin gwamnati ba ta dauki mataki ba, hakan zai rage yawan kayan abinci da ake nomawa a jihar. Malam Abdurrahman ya kara da cewa, abin bakin ciki ne yadda manoma ke biyan kudin fansa ga ’yan ta’adda kafin a bari su yi shuka ko girbe abin da suka noma a kasa irin Najeriya.

kaura da manoma ke yi zuwa gefen hanya abin damuwa ne – kungiyar Manoma

Shugaban kungiyar Manoma ta kasa (AFAN) a Jihar Kaduna, Alhaji Kabir Saleh ya nuna damuwarsa kan yadda manoma ke kaura zuwa gefen hanya ko kusa da gari.

Sai dai a cewarsa matsalar ba a dukkan kananan hukumomin jihar ba ne, illa a kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro da ba su wuce shida ba.

Ya bukaci gwamnati ta umarci jami’an tsaro su yi dukkan mai yiwuwa wajen korar ’yan ta’addan daga kauyukan da suke kusa da dazuka domin manoma su samu damar komawa gonakinsu.

“Muna matukar bukatar tsaro ga manoma a yayin da suke shirin komawa gonakinsu domin fara shuka. Saboda yin shuka a gefen hanya ba zai taimaka mana wajen magance matsalar abinci ba.

Dole ne jami’an tsaro su taimaka wurin korar ’yan bindiga daga garuruwan da suke gefen daji don taimaka wa manoma su koma gonakinsu,” inji shi.