✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Yadda fasinjoji suka kaurace wa hanyar Kaduna zuwa Abuja

Direbobin motocin haya dake bin babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sun koka kan karancin fasinjoji saboda yadda ake kauracewa hanyar don tsoron masu garkuwa da…

Direbobin motocin haya dake bin babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja sun koka kan karancin fasinjoji saboda yadda ake kauracewa hanyar don tsoron masu garkuwa da mutane.

Aminiya ta gano cewa matsalar garkuwa da mutane da ta ‘yan bindiga ta dada kamari a hanyar a ‘yan kwanakin nan.

Abdulsalam Abubakar, wani direban mota a tashar Zuba da kuma yake bin hanyar a kai a kai ya ce ana samun karancin fasinjoji tun dawowar ayyukan ‘yan bindigar a hanyar.

Ya ce karancin na zuwa ne a daidai lokacin da suke kokarin murmurewa daga matsalar tsadar man fetur da kuma annobar COVID-19.

A cewarsa, “Mun ga karin jami’an tsaro dake ta sintiri tun daga Zuba har zuwa Kaduna amma duk da haka fasinjojin ba sa son zuwa, sun tsorata matuka.

“Mu kan shafe sa’o’i da dama kafin mu cika ko da mota daya saboda karancin fasinjojin. Fata na shine hukumomi su yi abinda ya dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar matafiyan,” inji Abdussalam.

Wani direban mai suna Bello Murtala ya ce ya kawo fasinjoji daga Kaduna bayan shafe sa’o’i masu yawa a tasha.

Ya ce, “Na dauko su ne daga tashar mota ta Abuja Junction dake Kaduna zuwa Zuba Garage, gaskiya ziga-zirga ta ragu matuka a kan hanyar nan.

“Duk da yake akwai jami’an tsaro musamman a Gidan-Busa, inda aka yi garkuwa da wasu ranar Lahadi. Ba mu saba ganin abinda ya faru ba, mutane ba ma sa son yi wa juna magana, wasu kuma su kan yi shiru suna addu’ar sauka lafiya.

“Yanzu kwata-kwata ba ma cin riba; ga tsadar mai ga kuma karancin fasinjoji, amma muna fatan abubuwa su daidaita,” inji shi.

Shi kuwa a nasa bangaren, wani direban, Ahmadu Baba ya ce yanayin ya tilasta musu kara kudin mota.

Ya ce, “Ina karbar N5,000 daga Abuja zuwa Kano. Da N4,000 mu ke karba a karamar mota, N3,500 kuma a motocin bas-bas.

“Ba damar ka zo Abuja ka koma ranar saboda babu fasinjoji a kasa, yanzu sun gwammace su tafi ta jirgin kasa,” inji shi.

Fasinjoji sun koma tururuwa a tashoshin jiragen kasa

Binciken Aminiya ya gano cewa fasinjoji kan yi tururuwa zuwa tashoshin Idu da Kubwa dake Babban Birnin Tarayya Abuja domin zuwa Kaduna.

Wasu fasinjoji dake son tafiya zuwa Kano da Jigawa da Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma wadanda ke zuwa jihohin Arewa maso Gabas kamar Borno da Yobe su ma su kan bi jirgin zuwa Kaduna daga nan sai su hau mota zuwa jihohinsu.

A ziyarar da muka kai tashoshin jiragen biyu, wakilanmu sun iske dimbin mutane da iyalansu na kokarin tafiya Kaduna.

Yawancinsu dai kan zo a manyan motocin alfarma, yayin da wasu kuma har jami’an tsaro ne ke musu rakiya zuwa wurin.

Kazalika, su kan tanadi wasu mutanen da ke zuwa tarbarsu a Kaduna.

“Ba zan jefa rayuwa ta cikin hatsari ta hanyar tafiya ta mota ba,” inji Monica Jasfa, wata ‘yar kasuwa da za ta tafi Kano.

“Zan iya yin karin kudi ma domin in sami tikitin jirgin ko ma in daga tafiyar in na ga ba zan samu ba,” inji ta.

Shi kuwa wani Injiniya mai suna Shehu Adamu cewa ya yi amfani da jirgin ya fi dadi da kuma lafiya.

“Ko lokacin da ba kalubalen tsaro, na gwammace na tafi ta jirgin saboda rashin kyan hanyar. Zan tafi Kano amma na gwammace na ya da zango a Kaduna inda dan uwa na ke jira na,” inji shi.

Wani ma’aikacin tashar jirgin da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce fasinjoji masu karamin karfi sun kaurace wa tashar tun bayan dawowa da aikinta saboda tsadar tikitin.