✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan sa kai na neman cin karensu ba babbaka a Kebbi’

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yi gargadin cewa wata kungiyar ’yan daba da ake kira da ‘’Yan Sa Kai’ sun yi barazanar kashe…

Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya yi gargadin cewa wata kungiyar ’yan daba da ake kira da ‘’Yan Sa Kai’ sun yi barazanar kashe wadanda za su nada sabon Hakimin Bajida a Karamar Hukumar Fakai ta jihar.

Gwamnan ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci ayyukan da za su kai ga gurgunta zaman lafiyar jihar ba.

A watan Agusta ne wasu ’yan bindiga suka yi wa Hakimin na Bajida, Alhaji Muhammad Bahago kisan gilla, wanda haka ya samar da gurbin da ke bukatar nada wanda zai maye gurbinsa.

Gwamna Bagudu wanda ya yi gargadin a karshen mako yayin wata tattaunawa a Birnin Kebbi ya ce gwamnati ba za ta zauna ta kyale batagari su salwantar da zaman lafiyarta ba.

Ya ce, “A jiya-jiyan nan lokacin ana tsaka da tattaunawa kan yadda za a zabi zabon hakimin gundumar Bajida, wasu ‘yan kungiya da ake kira da ‘yan sa kai su ka kewaye wurin taron tare da barazanar kashe kowa muddin su ka sake su ka zabi wani.

“Na yi gargadin cewa gwamnatin jiharmu ba za ta zaune ta nade hannuwa ta kyale wasu bata gari, makiya zaman lafiya su yi mana illa ba. Ba za mu kyale rashin mutuncin da ya kai ga sanadiyyar kashe tsohon hakimi ya ci gaba da faruwa ba.

“Gwamnati na yi gargadi da kuma kira da babbar murya kan kada wata al’umma ta dauki doka a hannunta ko ta kirkiri wani gungun jama’a da za su dauki makamai,” inji gwamna Bagudu.