✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar wutar Lantarki: Ganduje zai yi rusau a Kano  

Hakan ya biyo bukatar Ministan Lantarki a Kanon

Akwai yiwuwar Gwamnatin Jihar Kano ta rushe gidajen da aka gina a karkashin babbar hanyar wutar lantarki a bisa bukatar Ministan Lantarki.

Hakan ta fito fili ne yayin da Ministan, Injiniya Abubakar D. Aliyu ya kai ziyarar gani da ido na aikin samarwa da kuma inganta wutar lantarki a jihar.

Ministan wanda ya kewaya tasoshin rarraba wutar lantarki na Dan Agundi da Rimin Zakara ya koka da yadda gine-ginen da ake yi ba bisa ka’ida ba a kan hanyoyin lantarki ke kawo cikas a aikin inganta wutar a Kano.

A nashi jawabin, Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, zai duba lamarin.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen mayar da Kano wata babbar cibiya ta rarraba wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

Don haka ya ce gwamnatin take son kara yawan karfin wutar lantarki da Kano take samu zuwa megawatt 2,000, karkshin wani shiri tare da hadin gwiwar kamfanin Siemens na Jamus

Yayin ziyarar, Ministan ya zagaya tashar lantarki ta Dan Agundi, inda ya roki Gwamnan da ya sa baki domin ganin cewar an kawar da gidajen da suka yi kutse a karkashin layin lantarki musamman daga Kumbotso zuwa Dan Agundi,