✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsin tattalin arzikin da duniya za ta fada a 2023 zai zarce na 2022 — IMF

Matsin tattalin arziki a 2023 zai zarce na 2022 — IMF

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), ya yi gargadin cewa shekarar 2023 da muka shiga za ta kasance mai tsaurin gaske ga tattalin arzikin duniya.

Asusun ya ce za a fuskanci barazanar ce sakamakon kalubalen da Amurka da kungiyar Tarayyar Turai da kuma China suke fuskanta, na raunin da karfin tattalin arzikinsu ke yi.

Shugabar Asusun IMF, Christalina Georgieva ta ce sabuwar shekarar da aka shiga za ta kasance mafi tsauri a kan 2022 da ta gabata.

A watan Oktoban 2022, Asusun IMF ya rage girman hasashen ci gaban da tattalin arzikin duniya zai samu a shekarar 2023, saboda tasirin yakin Rasha da Ukraine, da hauhawar farashin kayayyaki da kuma yawan kudin ruwa da manyan bankunan kasashe ke karawa kan basussukan da suke bayarwa.

A baya bayan nan, kasar China ta kawo karshen dokokin takaita walwala da ta shafe fiye da sekara biyu tana aiki da su, domin dakile yaduwar cutar Kwarona.

Ta yi hakan ne da niyyar sake farfado da tattalin arzikinta.

Sai dai duk da haka masu hada-hadar cinikayya sun ci gaba da yin taka-tsantsan, ganin yadda cutar Kwarona ke karuwa a tsakanin al’ummar kasar.

Yayin da take karin bayani kan makomar tattalin arzikin China, Shugabar Asusun IMF ta ce a karon farko cikin shekara 40, ci gaban da kasar China ta samu a shekarar 2022 zai iya zama koma-baya ko kuma kasa da matakin da ya kamata a ce ya kai.

Haka kuma yaduwar cutar Kwarona da karuwar masu fama da cutar a cikin watanni masu zuwa, na iya yin illa ga tattalin arzikin China a bana, tasirin hakan kuma na iya bazuwa zuwa sassan duniya.