Matukiyar jirgin yaki ta farko a Najeriya ta rasu | Aminiya

Matukiyar jirgin yaki ta farko a Najeriya ta rasu

Marigayiya Tolulople Arotile
Marigayiya Tolulople Arotile

’Yar Najeriya ta farko mai tuka jirgin yaki mai saukar ungulu, Tolulope Arotile ta rasu sakamakon hatsarin mota a jihar Kaduna.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya Ibikunle Daramola, a cikin wata sanarwa, ya ce Tolulope ta rasu ne sakamakon raunin da ta samu a kanta, a hatsarin na ranar Talata.

“A dan zamanta a rundunar, Marigayiya Tolulope ta taka muhimmiyar rawa ta hanyar tuka jiragen yakin rundunar ‘Operation Gama Aiki’ wajen yakar ’yan bindiga da sauran miyagu, a jihar Neja, da ke Arewa ta Tsakiya”, inji shi.

Sanarwar ta bayyana jimami tare da mika ta’aziyyar Babban Hafsan rundunar, Sadique Abubakar da daukancin jami’an rundunar ga dangin marigayiyar.

Tolulope, ’yar asali jihar Kogi, ita ce mace ta farko ‘yar Najeriya ta da fara tuka helikwafta bayan an yaye daga kwalejin horas da kanan hafsoshin soji (NDA) da ke Kaduna a shekarar 2017.