✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidi: Ku zo mu hada hannu mu yaki rashawa —Buhari

Shugaban ya yi wannan kira ne a sakonsa na Mauludi ga al’ummar Musulmi

Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan Najeriya da su hada hannu da gwamnatinsa a kokarin da take yi na yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaban ya yi wannan kira ne a sakonsa na Mauludi ga al’ummar Musulmin kasar ta hanyar wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a.

Shugaban ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kula da hakkin mata da yara da kuma girmama su, sannan su rika mutunta juna.

A cikin sakon, Shugaba Buhari ya yi kira ga ’yan siyasa da su guji amfani da miyagun kalamai ga junansu, su kuma guji  cin zarafi da mutuncin juna, duk da nufin kaskantar da abokan siysarsu.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’un Fiyayyen Halitta, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda saboda kyawawan halayensa ne  mutane da yawa suka karbi Musulunci.

Daga karshe ya jaddada aniyarsa na tabbatar da an gudanar da zabe mai ingancin da salama a shekarar 2023.