✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidi: Obaseki ya taya Musulman Edo murna

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W). Obaseki ya…

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ja hankalin Musulman jihar a kan su ci gaba da koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (S.A.W).

Obaseki ya bayyana haka ne cikin jawabin taya murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da ya ke gudana a ranar Alhamis.

Obaseki ya ce, “Ina taya Musulmai maza da mata na jihar Edo da ma kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

“A wannan rana muna kira da Musulmai mu ci gaba da nuna kauna da zaman lafiya, domin cigaban jiharmu da kasa baki daya”, inji shi.

Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da zama makwabta nagari kamar yadda Ma’aikin ya koyar.

Daga nan sai ya yi kiran samun hadin kan mutanen jihar domin wanzuwar zaman lafiya.