✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rarara ya raba wa ma’aikatansa kyautar gida da mota

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje dogarinsa da kyautar mota kirar Golf 4. Darakta Aminu S. Bono ya bayyana hakan, inda ya rubuta…

Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje dogarinsa da kyautar mota kirar Golf 4.

Darakta Aminu S. Bono ya bayyana hakan, inda ya rubuta cewa, “Ciyaman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje Abdullahi A. Abdullahi wanda aka fi sani da scorpion kuma daya daga cikin dogaransa da kyautar mota kirar Golf 4.

“Scorpion ya yi farin ciki sosai sannan kuma ya yi wa ciyaman Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara godiya tare da addu’ar Allah Ya raba shi da mahaifiyarsa lafiya.”

Scorpion a cikin motar da aka ba shi

Aminiya ta ruwaito cewa Rarara ya ba da kyautar motoci da dama a Masana’antar Kannywood a baya.

A wani labarin daban, Rarara ya ba Lirwanu Usman wanda aka fi sani da Aci Halak, wanda daya ne daga cikin ma’aikatansa na ofis kyautar gida.

Lokacin da Rarara yake mika takardun gidan ga Aci Halak