✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Al-Shabaab sun kashe mutum 8 a otel a Somaliya

Mayakan kungiyar Al-Shabaab sun hallaka fararen hula akalla takwas a wani otel da ke Mogadishu, babban  birnin kasar Somaliya.

Mayakan kungiyar Al-Shabaab sun hallaka fararen hula akalla takwas a wani otel da ke Mogadishu, babban  birnin kasar Somaliya.

Hukumomin kasar sun ce mayakan sun yi garkwua da mutane da dama a otel din Al-Hayat, inda jami’an gwamnati da manyan mutane ke yawan gudanar da taruka.

Wani kwamandan tsaro, Mohamed Abdikadir, ya ce, “Jami’an tsaro sun yi wa wurin kawanya kuma suna ci gaba da kawar da ’yan ta’addan, wadanda suka shige wani daki a otal din.

“An kubutar da yawancin mutanen da ke otel, amma fararen hula akalla takwas sun rasa rayukansu.”

A yammacin yararn Juma’a ne mayakan suka kutsa cikin otel din suna harbe-harbe da tayar da bama-bamai tare da yin garkuwa da mutanen da ke ciki.

A safiyar Asabar wani jami’in gwamantin kasar ya sanar cewa jami’an tsaro sun yi wa wurin kawanya da ’yan ta’addan suke kawanya domin murkushe shi.

Sai dai an yi ta jin karar harbi da fashewar bama-bamai har zuwa safiyar Asabar a otel din.

Harin dai shi ne mafi muni a Somaliya tun bayan zaben Shugaba Hassan Sheikh Mohamud, a watan Mayu, bayan rikicin siyasa a kasar.

Kungiyar Al-Shabaab dai ta dauki alhakin hare-haren da aka shafe sama da shekara 15 ana kai wa gwamnatin kasar.