✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Ansaru sun kashe ’yan bindiga 30 a Kaduna

Bangarorin suna fada a yayin da suke neman danne juna a yankin Birnin Gwari.

Akalla ’yan bindiga 30 sun sheka lahira bayan wani fada da suka gwabza da mayakan kungiyar Ansaru a yankin Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Majoyoyinmu a yankin sun tabbatar cewa fadan ya kaure tsakanin bangarorin ne a kokarinsu na nuna karfin iko a kan juna a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar Birnin Gwari, Hassan Ibrahim, ya ce, “Bangarorin biyu na ci gaba da karkashe juna amma an samu raguwar satar mutane; Yanzu ’yan ta’addar sun fi mayar da hankali a kan yadda za su samu fetur da kudade a hannun matafiya.

“Ko shekaranjiya sai da suka tare wani dan uwana a hanyar Birnin Gwari zuwa Zariya suka zuke man duk man da ke cikin babur dinsa, suka kwace masa waya da kudade sannan suka kyale shi. Ina ganin sabbin matakan tsaron da aka dauka suna aiki,” inji shi.

Rikicin na ’yan bindiga da mayakan Ansaru da aka fara a makon jiya na zuwa ne kimanin mako uku bayan ’yan ta’addar da sojoji suka fatattaka daga Jihar Zamfara sun fara neman mafaka a kauyukan Saulawa da Damari a karamar hukumar, inda suka kafa tutarsu.

Da yake mana karin haske game da lamarin, wani dan asalin Birnin Gwari da ke zaune a Zariya, ya ce fadan ya kaure ne bayan kungiyar Ansaru ta kafa dokar haramta wa ’yan bindiga yin garkuwa da mutane ko kai wa kauyuka hari.

Ya ce bayan ’yan bindiga sun yi kunnen uwar shegu da umanrin na mayakan Ansaru ne fada ya kaure a tsakanin bangarorin, har aka kashe ’yan bindiga hudu da dan kungiyar Ansaru daya a ranar Talatar makon jiya.

Daga nan ne bangarorin suka fara kai wa juna harin ramuwar gayya, wanda a makon jiya Ansaru ta kashe ’yan bindiga akalla 30.

Shugaban Karamar Hukumar Birnin Gwari, Hassan Ibrahim, ya ce a baya kungiyar ta yi wa ’yan bindiga kashedi game da satar mutane, amma taurin kan ’yan bindigar ne ya haifar da fada a tsakanin bangaron.

Mun tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, a kan lamarin amma ya ce mu ba shi lokaci zai tuntubi DPO na yankin Birnin Gwari domin ya ji halin da ake ciki.

Sai dai kuma bayan wasu awanni mun sake kiran ASP Jalige, amma bai amsa kiran wayar tamu ba, har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.