✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram 50 sun mika wuya a Kamaru

Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, ake samun karuwar masu mika wuya.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram 50 sun mika wuya a garin Maro da ke Arewa mai nisa na Jamhuriyyar Kamaru.

A tsawon wata biyu kawo yanzu, akalla mayakan Boko Haram 183 suka ajiye makamansu da mika wuya ga mahukunta a Kamaru.

Shugaban Cibiyar Gyara Halinka a yankin Arewar, Oumar Bichair ya shaida wa BBC cewa, a kullum a adadin mutanen da yake karba da suka tuba na karuwa.

Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, ake samun karuwar masu mika wuya da neman tuba tsakanin mayakan.

Alkalumma sun nuna cewa, rikicin Boko Haram da ya samo asali tun a shekarar 2009, ya yi sanadiyar rayukan mutum dubu 13 da raba akalla mutum miliyan 1.5 da muhallansu.