✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun fara komawa dajin Kaduna —DSS

Mayakan sun fara sauya sheka zuwa dajin Rijana da ke Jihar Kaduna.

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci hukumomin tsaro a Jihar Kaduna da su kara kaimi wajen sa ido da tattara bayanan sirri saboda kwamandojin kungiyar Boko Haram na yin kaura daga Dajin Sambisa zuwa Kudancin Kaduna.

Rahotanni sun ce ’yan ta’addar sun fara yin kaura daga dajin Sambisa da ke Jihar Borno ne zuwa dajin Rijana da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Takardar sanarwar ta bayyana cewa wani babban kwamandan Boko Haram, Ibrahim, tare da tawagarsa na shirin komawa karkashin jagorancin Adamu Yunusu, wanda aka fi sani da (Saddiqu)

Hukumar ta DSS ta kuma umarci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) da ta tsaurara matakan tsaro a yankunan da aka ambata da tare da kasancewa a cikin shirin ko ta kwana.

A cewar sanarwar, an umarci NSCDC da ta kara sa ido da tattara bayanan sirri a yankunan da aka ambata, don samun rahoton wadanda ake zargin.