✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a Yobe

Mazauna yankin sun fantsama dazuka don tsira da rayukansu.

Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kaddamar da hari a garin Babbangida, hedkwatar Karamar Hukumar Tarmuwa, a Jihar Yobe.

Wata majiya a yankin ta tabbatar da cewa mayakan na can suna musayar wuta da dakarun sojojin da ke yankin.

A cewar majiyar, tuni mazauna yankin da dama suka fantsama cikin dazuka don tsira da rayukansu.

“Yanzu haka muna cikin daji don tsira da rayuwarmu, na san yanzu ma haka kana jin karar harbe-harbe,” inji majiyar.

Harin dai na zuwa ne bayan an dan sami sassaucin yawan kai hare-haren mayakan Boko Haram da na ISWAP a yankin Arewa maso Gabas a ’yan kwanakin nan.