✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram sun kai hari Bauchi

Mayakan sun tsallaka jihar Bauchi ce daga Yobe da ke makwabtaka da ita.

Mayakan Boko Haram daga Jihar Yobe, sun tsallaka wasu Kananan Hukumomi hudu na Jihar Bauchi inda suka kone gine-gine da dama.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabi’u Baba ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai ranar Litinin a birnin Bauchi.

Ya wassafa sunayen Kananan Hukumomin da lamarin ya shafa da suka hada da Zaki, Gamawa, Darazo da Dambam.

Rahotanni sun bayyana cewa, mayakan sun lalata wasu turakun sadarwa a Karamar Hukumar Gamawa.

Alhaji Baba ya ce jami’an tsaro sun kama mutane biyar da ake zargi da wannan ta’adi, inda tuni gwamnatin jihar ta tsananta tsaro a dukkan yankunan da sauran masu makwabtaka da su.

Ya ce gwamnatin jihar ta gano da wani babban kalubale na tsaro a yayin da mutane ke ci gaba da kwararowa cikin jihar daga Yobe inda mayakan Boko Haram ke ta’asa.

A cewarsa, Gwamna Bala Mohammed ya samar da karin goyon bayan da jami’an tsaro ke bukata domin karfafa sintiri da sanya ido musamman a yankunan da ke kan iyaka da Jihar Yobe.

Dangane da batun ’yan hijira, Baba ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da al’ummomin da abin ya shafa domin gano wadanda suka rasa muhallansu domin ba su tallafin gaggawa da zummar rage musu radadin wahalar da suke ciki.

A nasa jawabin, Kwamishinan jihar, Sylvester Abiodun Alabi, ya ba da tabbacin cewa ’yan sanda za su yi aikin hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da aminci wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kazalika, ya nemi mazauna jihar da su rika bai wa jami’an tsaro bayanan da za su tallafa musu wajen kama bata-gari sannan kuma su guji rufa wa mutane masu mugun nufi asiri.