✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram sun kashe Kwamandan soji a sansanin dakaru a Borno

A makonnin baya bayan nan mayakan sun tsananta kai wa dakaru hari.

Mayakan Boko Haram sun kashe Kwamandan soji da wasu mutum bakwai yayin wani hari da suka kai sansanin dakaru biyu a Jihar Borno.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin dakarun da ke Ajiri, mai tazarar kilomita 20 daga Maiduguri, babba birnin Jihar Borno.

An yi ta musayar wuta ta tsawon sa’a biyu da safiyar Lahadi tsakanin dakarun soji da mayakan a wata tankar yaki da kuma wasunsu haye a kan babura, lamarin da ya tilasta dakarun suka ja da baya.

Kwamandan sansanin ya rasa ransa tare da wasu fararen hula shida da lamarin ya ritsa da su a cewar wata majiya ta dakarun sojin.

Majiyar ta ce, “wani farar hula da ya samu raunika daga bisani ya riga mu gidan gaskiya a gadon asibiti.”

Aminiya ta ruwaito cewa, makamancin wannan harin ya auku a daren ranar Asabar yayin da mayakan Boko Haram suka kai hari sansanin dakarun soji da ke garin Rann a jihar ta Borno.

Cikin makonnin baya bayan nan, mayakan sun tsananta kai wa sansanin dakarun soji hari a yayin da suke ci gaba da tumke damarar ta’addanci da suka kulla fiye da tsawon shekaru goma da suka gabata wanda ta janyo asarar rayukan sama da mutum 36,000.