✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru 2 a Borno

“Akwai sojojin Kamaru 2 da aka kashe yayin musayar wutar da ’yan ta’addan na Boko Haram.”

Wasu sojojin kasar Kamaru guda biyu da aka girke a Najeriya sun gamu da ajalinsu ranar Asabar bayan da wasu mayakan Boko Haram suka bude musu wuta, kamar yadda wasu majiyoyi a Rundunar Sojin Najeriya suka tabbatar.

’Yan ta’addan wadanda ke tafe a kasa, wasu kuma a kan motoci dauke da muggan bindigogi dai tun da farko sun kai hari ne kan sojojin Najeriya a garin Wulgo na jihar Borno.

Daga nan ne kuma sai suka kaiwa sojojin na Kamaru hari wadanda suke aikin taimako a kan iyakar Najeriya.

A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, wani sojan Najeriya ya ce, “Akwai sojojin kasar Kamaru guda biyu da aka kashe bayan musayar wuta ta kusan tsawon mituna 40 da ’yan ta’addan Boko Haram.”

“Sannan akwai wasu karin sojojin na Kamaru guda uku da na Najeriya daya da suka sami raunuka a musayar wutar,” inji wata majiyar ta daban daga cikin sojojin.

Kazalika, yayin ba-ta-kashin dai an lalata wata motar silke mallakar sojin Najeriya da kuma wasu motoci kirar igwa na Boko Haram guda biyu, sannan kuma an kashe musu mayaka da dama.

Mayakan dai sun kaddamar da harin ne a kusa da dajin Wulgo wanda sanannen mafaka ne ga ’yan ta’addan.

Yakin Boko Haram dai, wanda aka fara shi tun 2009 ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 36,000 sannan ya raba sama da miliyan biyu da muhallansu kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar.