✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Houthi sun harba makami mai linzami cikin Saudiyya

Saudiyya ta ce harin wani yunkuri ne na kawo cikas ne ga samar da makamashi a duniya.

’Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun harba makamai masu linzami tsakiyar ginin kamfanin man kasar Saudiyya, Aramco da ke birnin Ras Tanura ranar Lahadi.

Ma’aikatar Makamashi ta Saudiyya ta tabbatar da kai harin a kan wata matatar mai da kuma daya daga cikin wuraren ajiyar man mafi girma a duniya, ko da yake ba a sami asarar rai ko ta dukiya ko kadan ba.

Sanarwa ta ce, “Daya daga cikin tankokin mai a tashar jiragen ruwa ta Ras Tanura a gabashin kasar, wacce daya ce daga cikin manyan tashoshin ruwa a duniya ta fuskanci hari da makami mai linzami a ranar Lahadi.”

Saudiyya ta bayyana harin a matsayin yunkurin ’yan Houthin na kawo cikas ga kokarin samar da makamashi a duniya.

Ta kara da cewa makamin ya fada ne kusa da ginin kamfanin man kasar na Aramco da ke Dhahran.

“Wannan aikin ta’addancin ba wai iya Saudiyya kawai zai cutar ba, hatta yanayin samar da makamashi ga kasuwar duniya da ma tattalin arzikinta sai ya shafa,” inji kakakin ma’aikatar.

Da take sanar da kai harin, kungiyar Houthi ta ce ta kai wani harin kan sojojin Saudiyya a biranen Dammam da Asir da kuma Jazan.

Kakakin kungiyar ta Houthi, Yahya Sarea ya ce sun harba jirage mara sa matuka guda 14 da kuma makamai masu linzami guda takwas kusa da kan iyakar Yemen da Saudiyya a wani abin da suka kira babban hari a tsakiyar kasar.

Birnin da aka kai harin dai shi ne inda akasarin gine-ginen kamfanin man Saudiyya na Aramco suke.

Kakakin rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ’yan tawayen Houthi a Yemen ya ce Saudiyya za ta dauki dukkan matakan da suka kamata wurin kare kanta da kuma tabbatar da ci gaba da samar da wadataccen makamashi ga sauran kasashen duniya.