✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan ISWAP sun harbe Birgediya Janar a Borno

A yau rana ce ta bakin ciki a gare mu da muke nan filin daga.

Mayakan ISWAP sun harbe wani Birgediya Janar din soji a wani hari na kwanton bauna da suka kai Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa an kuma kashe wasu sojoji hudu yayin harin da ya auku a Bulguma, wani yanki mai tazarar kilomita kadan da garin Askira na Karamar Hukumar Askira Uba da ke Borno.

Bayanai sun ce mayakan sun yi wata rundunar hadin gwiwa daga garin Chibok kwanton bauna da aka tura dakarunta domin kai dauki yankin da lamarin ya faru.

Aminiya ta ruwaito cewa, mayakan sun yi wa garin Askira dirar mikiya ne da misalin karfe bakwai na safiyar Asabar a cikin jerin gwanon motoci, suna luguden wuta babu kakkautawa.

Wata majiya ta ce “yau rana ce ta bakin ciki a gare mu da muke nan filin daga, domin kuwa mun rasa babban Kwamanda mai mukamin Birgediya Janar.

“Birgediya Janar din da sojoji hudu sun rasa rayukansu yayin da suke kai hanyarsu ta kai wa sojoji dauki a garin Askira da mayakan ISWAP suka yi wa dirar mikiya,” a cewar majiyar.

Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun rundunar sojin kasa na Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a yammacin Asabar, ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici

Ya ce Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya jajanta wa iyalan sojojin da suka riga mu gidan gaskiya a harin.

Kazalika, ya bayyana Birgediya Janar Dzarma Zirkusu a matsayin sunan babban hafsan da aka kashe, sai dai ya yi shiru game da sunayen sauran sojojin da karar kwana ta cimmasu.

Wasu rahotanni sun ce mazauna yankin sun sanar da hukumomi game da shigowar mayakan amma ba a dauki mataki ba har suka fara bude wuta da misalin karfe 9 na safe.

Wani jami’in tsaron sa-kai a garin, Yakubu Luka, ya ce mayakan sun kai farmaki a wani sansanin soji ne da ke Askira.

“Muna jira a kawo mana karin mutane daga garuruwan da ke kusa da mu, yanzu hakan rugugin harbi ne a ko’ina a garin.

“Muna kira da a turo jiragen yaki su taimaka wa dakarun da ke kasa, maharan sun fi mu yawa, motocin yaki biyar kawai gare mu,” inji Yakubu.