Mayakan ISWAP sun sace jami’an gwamnati 5 a Borno | Aminiya

Mayakan ISWAP sun sace jami’an gwamnati 5 a Borno

Wasu mayakan ISWAP
Wasu mayakan ISWAP
    Olatunji Omirin, Maiduguri da Sani Ibrahim Paki

Akalla jami’an Gwmnatin Jihar Borno su biyar da ke rangadin duba ayyuka ne mayakan kungiyar ISWAP suka yi garkuwa da su a ranar Laraba.

Jami’an dai sun gamu da iftila’in ne yayin da suke duba aikin hanyar Chibok zuwa Damboa, inda aka kwashe su ta karfin tsiya.

Lamarin dai ya faru ne kusa da Wovi, wani kauye da ke Karamar Hukumar Chibok.

Wata majiya daga yankin ta tabbatar wa da Aminiya cewa wani daga cikin jami’an da ma direban motar sun samu nasarar tserewa ba tare da jin rauni ba.

Kazalika, wani babban jami’i a Gwamnatin Jihar ya tabbatar wa Amniya cewa, “Eh, gaskiya ne, kuma wannan abin takici ne matuka.

“Lamarin ya zo mana da ba-zata. Tabbas an sace su yau da safe,” inji majiyar.